Bankin duniya ya bawa tsohon minista, Muhammad Pate, babban mukami

Bankin duniya ya bawa tsohon minista, Muhammad Pate, babban mukami

Bankin Duniya ta nada Muhammad Ali Pate, tsohon karamin ministan lafiya na zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a matsayin direktan lafiya, samar da abinci da kidaya na duniya.

An kuma nada Pate a matsayin direktan 'Global Financing Facility' (GFF) na kungiyar Bankin Duniyan.

A sakon taya murna da ya wallafa a ranar Laraba, Direkta Janar na Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus ya ce yana fatan yin aiki tare da Pate a nan gaba.

Bankin duniya ya bawa tsohon minista, Muhammad Pate, babban mukami

Bankin duniya ya bawa tsohon minista, Muhammad Pate, babban mukami
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

"Ina taya ka murna @muhammadpate bisa tabbatar da kai da Bankin Duniya tayi a matsayin Direktan Lafiya, Samar da abinci da Kidiya na kungiyar Lafiya ta Duniya na GFF. Muna fatan yin aiki tare da kai domin cimma muradan mu," kamar yadda Ghebreyesus ya rubuta a Twitter.

A watan Yulin 2013 ne Pate ya yi murabusa a matsayin karamin Ministan Lafiya na Najeriya domin fara aiki a matsayin Farfesa a Cibiyar Lafiya ta Jami'ar Duke da ke kasar Amurka.

A baya, kwararen likitan ya yi aiki da a matsayin jagoran bangaren inganta al'umma na Gabashin Asia da Yankin Pacific da kuma babban kwarare a yankin Afirka na Bankin Duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel