Aikin Umrah: Jirgin Buhari ya lula zuwa kasar Saudiyya

Aikin Umrah: Jirgin Buhari ya lula zuwa kasar Saudiyya

- Jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya

- Shugaban kasar zai je yin aikin Umrah ne a kasa mai tsarki

- Tafiyar nasa ya biyo bayan gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz, wato Sarkin Saudiyya da wakilan masallatai masu tsarki biyu suka masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga wata Mayu ya tashi daga filin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa jirgin Shugaban kasar ya kwashi Buhari da tawagarsa daga filin jirgin da misalin karfe 11:00 na safe.

Wadanda suka je filin jirgin don sallamar Shugaban kasar sun hada da Shugaban ma’aikata, Malam Abba Kyari; ministan birnin tarayya; mukaddashin Shugaban yan sandan Najeriya, Muammed Adamu da kuma sauran jami’an gwamnati.

Aikin Umrah: Jirgin Buhari ya lula zuwa kasar Saudiyya

Aikin Umrah: Jirgin Buhari ya lula zuwa kasar Saudiyya
Source: Twitter

An tattaro cewa tafiyar Shugaban kasar zuwa kasa mai tsarki ya biyo bayan gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz, wato Sarkin Saudiyya da wakilan masallatai masu tsarki biyu suka masa.

A wani jawabi daga babban mai ba Shugaban kasar shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, a Abuja a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa shugaba Buhari zai yi aiki Umrah a yayinda ya je masarautar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na karbi sarautar Sarkin Bichi daga hannun Ganduje – Aminu Ado Bayero

Shugaba Buhari yayi Umararsa ta karshe a watan Fabrairun 2016.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel