An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

Rundunar 'yan sanda a jihar Edo, a ranar Alhamis, ta ce ta kama wasu kama mutane hudu da take da kyakyawan zaton cewar mayakan kungiyar Boko Haram ne da suka gudu daga jihar Kogi bayan sun tafka aiyukan ta'addanci.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed DanMallam, ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Benin.

DanMallam ya ce an kama mutanen ne bayan samu bayanan sirri a kan wata maboyar su dake Afuze-Edo a sanatoriyar jihar Edo ta kudu.

Ya bayyana cewar, a yayin da masu laifin ke amsa tambayoyi, daya daga cikin su ya amsa cewar ya kashe mutane fiye da 40, yayin da daya daga cikin su ya ce ya gudu ne daga gidan yarin Koton Karfe a shekarar 2014, sannan yana daga cikin wadanda suka yi fashi a jihar Ekiti a shekarar 2013.

An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

'Yan sanda
Source: UGC

Ya kara da cewa zasu mika masu laifin hannun rundunar 'yan sanda a jihar Kogi domin zurfafa bincike a kan irin aiyukan ta'addanci da suka tafka a jihar.

DanMallam ya shaida wa NAN cewar rundunar 'yan sandan jihar ta samu gagarumar nasara ta fuskar yaki da aiyukan ta'addanci da miyagun laifuka tun bayan kaddamar da atisayen 'Puff Adder'.

DUBA WANNAN: An kama wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan Katsina

Ya bayyana cewar an kama masu laifi 34 dake da alaka da aikata laifin fashi da makami da kuma wasu mutum hudu da ake dake da hannu a garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa an kama 'yan kungiyar asiri 32 da kuma samun nasarar kama makamai da dama daga hannun masu laifi daban-daban da aka kama.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce sun kubutar da a kalla mutane 9 daga hannun masu garkuwa da mutane, yayin da suka kwace motoci 11.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel