Yanzu Yanzu: Mataimakin kakakin majalisar dokokin Imo yayi murabus

Yanzu Yanzu: Mataimakin kakakin majalisar dokokin Imo yayi murabus

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Ugonna Uzuruigbo, ya yi murabus. Dan majalisar mai wakiltan yankin Nwangele a jihar ya mika wasikar ajiye aikinsa a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Shi da kansa ya sanya hannu a wasikar. Ya mika ta zuwa ga kakaki da mambobin majalisar dokokin jihar.

Ozuruigbo yayi bayani a wasikarsa cewa yayi murabus ne domin ya samu damar aiki sosai a matsayin zababben mamba a majalisar dokokin kasar.

Yanzu Yanzu: Mataimakin kakakin majalisar dokokin Imo yayi murabus

Yanzu Yanzu: Mataimakin kakakin majalisar dokokin Imo yayi murabus
Source: UGC

“Kamar yadda kuka rigada kuka sani, mazabata ta sake tura ni wani aikin shekaru hudu a majalisar tarayya, domin na wakilce ta a majalisar dokokin kasa, Abuja.

“Wannan sabon aiki ya zo da kalubalensa da hangen nesa, musamman wajen bukatar taka muhimmin rawa a wajen zabar shugabancin majalisar dokoki, kuma lokaci yayi da za a nemi hakan domin ra’ayin jihar Imo, kudu maso gabas da kuma Najeriya, a majalisar tarayya. Yanzu haka, wannan zai sa b azan dunga kasancewa a jihar Imo ba a koda yaushe.

KU KARANTA KUMA: Shettima ya goyi bayan Ganduje kan nadin sabbin sarakuna a Kano

“Don haka ina son kare ofishin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo ta hanyar yin murabus ko kuma na bari abubuwa su sha kasha a ofishin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar ta hanyar ci gaba da rike matsayin.

“Don haka, domin mutanen Imo masu alkhairi, na ajiye aiki a matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo (majalisa ta takwas), daga ranar da ke rubuce a sama,” kamar yadda yake a wasikar ajiye aikin."

Ajiye aikin mataimakin kakakin majalisar na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan yan majalisar jihar 21 cikin 27 sun mika takardar yunkurin tsigewa ga kakakin majalisar, Acho Ihim da Shugaban masu rinjaye Lugard Osuji, bayan dakatar dasu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel