Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan

Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan

Yan sandan shari’ar musulunci a jihar Kano sun tsare mutane 80 bisa zargin cin abinci a bainar jama’a a watan ramadana yayinda aka hana musulmai daga ci da sha daga billowar alfijir har zuwa faduwar rana a watan azumin.

Yan sandan shari’an wadanda aka fi sani da Hisbah, sun ce an kama mutanen ne a yankuna daban-daban a fadin birnin Kano cikin wasu yan kwanaki da suka gabata.

Jihar Kano ta kasance daga cikin jihohi da dama a yankin Arewa inda aka sake gabatar da dokar shari’a tun 2000. Ana zartar da Dokar shari’a ba tare da saba ma dokar kasar ba.

Kakakin Hisbah a jihar Kano, Adamu Yahaya, ya bayyana wa manema labarai cewa duk wadanda aka kama musulmai ne kuma jami’an hukumar basu taba wadanda ba musulmai ba saboda dokar musulunci bata shafe su ba.

Yace wadanda aka kama sun fada ma ofishin hukuman shari’an cewa suna cin abinci ne saboda basu ga watan Ramadan ba, sannan sauran sun ce suna fama da rashin lafiya, amman hukumar bata dauki dalilansu da muhimmanci ba.

Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan

Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan
Source: Twitter

Yahaya ya kara da cewa an gargade su sannan aka sake su saboda sun kasance “masu laifi a karo na farko.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mataimakin kakakin majalisar dokokin Imo yayi murabus

An kuma gargade su cewa idan aka sake kama su da laifi, za a gurfanar dasu a kotu. Hukumar Hisbah ta ce zata cigaba da gudanar da ayyukanta a cikin watan ramadan da niyyan kama musulmai wadanda basu azumi.

Azumin watan Ramadan dole ne akan dukkan balaggaggun musulmai amman azumin bai wajaba akan masu fama da rashin lafiya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel