Umahi zai bincki yadda VIO na karya su ka kashe wani tsoho a Ebonyi

Umahi zai bincki yadda VIO na karya su ka kashe wani tsoho a Ebonyi

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yayi Allah-wadai da kashe wani Dattijo da aka yi a jiharsa a cikin ’yan kwanakin nan. Gwamnan ya bayyana wannan ne a Ranar Talata 14 ga Watan Mayun 2019.

Yanzu haka gwamnan na Ebonyi ya bada umarni ayi bincike domin gano yadda akak kashe Sakataren majalisar dattawa na jihar watau Cif Geoffery Mgbada. Wasu ne su kayi shigan Jami’an VIO su ka kashe wannan Bawan Allah.

Kafin mutuwar Geoffery Mgbada, shi ne shugaban da ke kula da hukumar Abakaliki Capital Territory Development Board na babban birnin jihar. Wannan ya sa gwamnan jihar ya nemi a binciki yadda aka kashe wanann Dattijon.

Jaridar Southern City News tace wani sojan gona na VIO masu kula da motoci ne yayi sanadiyyar mutuwar Geoffery Mgbada. Wannan jami’in bogin ya fadowa Marigayin ne a kan titin Presco-Ezza lokacin da yake tuki a mota.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya goyi bayan Ganduje a kan kirkiro Masarautu

Karin bayanai sun nuna cewa wannan Jami’i da ya kashe Sakataren majalisar dattawan jihar Ebonyi, ya tsaya a kan titi ne da nufin karbar na-goro daga hannun Bayin Allah. Hadarin ya faru ne a cikin Garin Abakaliki a safiyar Talata.

A lokacin da wannan abu ya faru, Geoffery Mgbada, yana tare ne da Mai dakinsa a cikin mota. Tuni dai gwamnatin Ebonyi ta bakin babban Sakataren gwamna, Emmanuel Uzor, ta fito tayi tir da wannan abu da ya faru a mako nan.

Gwamna Umahi ya sa a gudanar da bincike domin gano gaskiyar wannan lamari. Tuni dai jami’an ‘yan sanda su ka kama wannan sojan gona da su ka jawo hadarin, su kayi ram da su, sannan aka kai gawar mamacin zuwa asibiti.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel