Shettima ya goyi bayan Ganduje kan nadin sabbin sarakuna a Kano

Shettima ya goyi bayan Ganduje kan nadin sabbin sarakuna a Kano

- Gwamna Kashim Shettima ya goyi bayan nada sabbin sarakuna a Kano

- Shettima ya tambayi ko akwai wani abu na musamman ne gane da nadin sabbin sarakunan

- Wata babbar kotun jihar da ke zama a Ungogo ta kaddamar da lamarin a matsayin hambararre

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shetima ya nuna goyon baya ga takwaransa na jihar Kano Umar Ganduje, inda yake bayyana cewa “menene abu na musamman game da sarkin saboda Allah?”

Shettima ya bayyana matsayarsa ne a lokacin da kwamitin sojoji suka ziyarce shi a Gidan Gwamnatin Borno a matsayin cikon ayyukan ta.

Gwamnan wanda ke shirin barin kujerarsa nan da makonni biyu masu zuwa, ya bayyana damuwar shi cewa a kulla yaumin zaka samu yankin Arewacin Najeriya a labarai akan dalilan da basu dace ba, bayan akwai muhimman al’amuran da ya kamata kowa ya mayar da hankali a kai.

Shettima ya goyi bayan Ganduje kan nadin sabbin sarakuna a Kano

Shettima ya goyi bayan Ganduje kan nadin sabbin sarakuna a Kano
Source: Facebook

Yace an kimanta cewa nan da 2050, kashi saba’in daga cikin al’umman Najeriya zasu kasance mazauna yankin arewa: “tare da kwararowar hamada, yanke-yanken itatuwa, talauci, rashin ilimi da yawan almajirai miliyan 12.”

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na karbi sarautar Sarkin Bichi daga hannun Ganduje – Aminu Ado Bayero

Shettima ya jadadda cewa ba za a taba samun zaman lafiya ba indan ba tare da ci gaba ba, sannan duba ga yadda matsaloli ke fuskantar yankin ya kasance babban dama na samar da damokradiyya. “ilimi ne babban makamin magance irin wadannan matsaloli,” a cewarsa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wata babbar kotun jihar da ke zama a Ungogo ta kaddamar da lamarin a matsayin hambararre.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel