Tsohon Gwamna Fayose ya soki Fayemi a kan shirin korar Ma’aikata a Ekiti

Tsohon Gwamna Fayose ya soki Fayemi a kan shirin korar Ma’aikata a Ekiti

Ana rade-radin cewa gwamnatin jihar Ekiti ta umarci a sallami ma’aikata 2000 da tsohon Gwamna Ayodele Fayose ya dauka aiki. Mun samu wannan labari ne a jiya Laraba 15 ga Watan Mayun 2019.

Ayodele Fayose yayi maza ya caccaki Gwamnan na APC bayan ya samu labarin take-taken na sa na sallamar dinbin Ma’aikatan da ya dauka aiki. Fayose yace tsabar keta da mugunta ce kurum a ran Gwamna mai-ci Fayemi.

Tsohon Gwamnan yayi wannan magana ne ta bakin babban Hadiminsa, Mista Lere Olayinka a Ranar Larabar nan. Lere yace akwai bita-da-kulli da gwamnatin Fayemi ta shiryawa wadannan Bayin Allah da Ayo Fayose ya samawa aiki.

KU KARANTA: Tinubu yana neman taimakon ‘Yan Majalisa a kan wani batu

Tsohon Gwamna Fayose ya soki Fayemi a kan shirin korar Ma’aikata a Ekiti

Fayose ya maida martani a kan korar Ma’aikata a Ekiti
Source: Depositphotos

A jawabin da Olayinka Lere ya fitar, yace Gwamna Kayode Fayemi yayi nasarar shiga tarihi a matsayin wanda ya gallazawa mutanen jihar Ekiti a dalilin raba su da hanyar neman abincin su, bayan gwamnatin baya ta rufa masu asiri.

Mai magana da yawun bakin tsohon gwamnan yake cewa an kori wadannan mutane daga aiki ne bayan gwamnatin baya ta bi duk matakai da sharudan da su ka dace kafin daukar su. Wannan dai zai kara yawan marasa abin yi a cikin jihar.

Fayose yake cewa a lokacin da gwamnatinsa ta dauki mutum 2000 ta ba aikin yi, ita kuma gwamnatin APC ta Kayode Fayemi, abin da tayi shi ne ta raba wadannan mutane da abin da su ke samu, da ta gaje sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel