An samu nasarar cafke karuwai da masu kaiwa 'yan bindiga rahoto a jihar Katsina

An samu nasarar cafke karuwai da masu kaiwa 'yan bindiga rahoto a jihar Katsina

Rundunar yan sanda ta kama Wasu mata hudu da ke kai rahoto, karuwanci da kuma dafa ma yan bindiga mazauna jejin Rugu abinci a jihar Katsina.

Wadanda aka kama a lokacin da rundunar yan sanda ta far musu a kauyen Runka dake karamar hukumar Safana dake jihar sun hada da Bilkisu Abubakar (24), Razika Amadi (25).

Rundunan tace, sauran sun hada da Zulai Dahiru (45) da Rakiya Yusufu (20) wadanda aka kama a kauyen Tudu, a lokacin da yan sandan suke gudanar aiki.

An samu nasarar cafke karuwai da masu kaiwa 'yan bindiga rahoto a jihar Katsina

An samu nasarar cafke karuwai da masu kaiwa 'yan bindiga rahoto a jihar Katsina
Source: Depositphotos

A lokacin da ake gurfanar da masu laifin, kakakin rundunar yan sanda a jihar, SP Gambo Isah yace masu laifin sun bayyana cewa suna kai rahoto, karuwanci da kuma dafa ma yan bindiga abinci a jejin. Sunayen yan bindigan da suke ma aiki sun hada da; Ruga Kachalla, Jume Basullube, Sumaye, Haruna Dun, Autan Kachalla, Yahuza Mai-Bakar Kama, Lawalli Adda, Babban Yara da Dogo.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina

“A wani lamari mai makamancin haka, Isah ya bayyana cewa an kama wani mai suna Nasiru Aminu (40) dake a kauyen Safana wanda ya kasance dan aike ga yan bindigan”.

Har ila yau, ya kara da cewa an kama wani Shuaibu Abubakar (40) na kauyen Tsamre a Birnin Magaji yayin da yake dauke da buhuna shida na kayan abinci da manja lita 25 a yayin da yake hanyar kai ma yan bindigan a jejin Rugu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel