Gwamnati na ta yi tasiri wajen inganta rayuwar al'umma a jihar Legas - Ambode

Gwamnati na ta yi tasiri wajen inganta rayuwar al'umma a jihar Legas - Ambode

Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode a jiya Laraba, 15 ga watan Mayun 2019, ya jaddada cewa gwamnatin sa ta yi tasirin gaske wajen inganta jin dadin rayuwar al'umma a tsawon shekaru hudu da ta shafe bisa kujerar mulki.

Cikin lafazin sa na bugun gaba, Gwamna Ambode ya ce gwamnatin sa ta hanyar habaka ci gaban gine-gine ta inganta jin dadin rayuwar al'ummar jihar Legas cikin tsawon shekaru hudu da ta yi akan gado na mulki.

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode
Source: Depositphotos

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, furucin gwamnan na zuwa ne yayin da yake kaddamar da wani katafaren aiki na ginin titi a wasu manyan hanyoyi uku dake yankin gundumar Ikotun-Igando a cikin birnin Legas.

Kazalika gwamna Ambode yayi kira tare da mika kokon barar sa na neman daukacin al'ummar jihar Legas da su kwatanta makamancin goyon baya da ya samu a gare su zuwa ga magajin sa, sabon zababben gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu.

KARANTA KUMA: Talakawa za su fara bore a Najeriya - Majalisa ta gargadi Buhari

Makonni uku da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Legas, inda ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba wanda gwamna Ambode ya aiwatar. Shugaba Buhari yayi furucin cewa hakika ya shaida gwamna Ambode ya sauke nauyin al'umma da rataya a wuyan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel