Tazarcen Buhari ta farkewa Obasanjo laya - Sarkin Legas

Tazarcen Buhari ta farkewa Obasanjo laya - Sarkin Legas

Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu ya ce nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu na zarcewa kan mulki karo na biyu babban hujja ce da ke nuna cewa Allah ne ke bayar da mulki ba mutum ba.

Akiolu ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin da daliban makarantar koyan dabarun mulki da tsaro (NIPSS), Kuru suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa daliban sun kai ziyarar karin ilimi ne karkashin Mukadashin Direktan NIPSS, Dr Nasirudeen Usman.

Akiolu ya ce shugaban kasar ya samu nasarar shi be daga Allah ta hannun jama'an Najeriya.

Ya ce ikirarin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi na cewa Buhari ba zai yi nasara ba saboda bai goyi bayansa ba ya fadi kasa banza bayan Buhari ya lashe zabe.

Nasarar Buhari ta farkewa Obasanjo laya - Sarkin Legas

Nasarar Buhari ta farkewa Obasanjo laya - Sarkin Legas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Akiolu ya ce Obasanjo ya dade yana daukan kansa a matsayin wanda ke zaban shugabanin Najeriya sai dai nasarar da Buhari ya samu a zaben 2019 ya farke masa laya kowa ya ganshi zigidir.

Akiolu ya ce dama ya yi imanin cewa Buhari ne zai lashe zabe kuma ya yi murnan ganin cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kunyatta.

"Dama na ce Buhari ne zai yi nasara tun kafin zabe, abin takaici babban wanda ya ke haifar da matsala a kasar nan shine Obasanjo.

"Ya bawa kansa iko irin na Allah yayin da ya ce goyon bayan da ya bawa Buhari ne yasa ya yi nasara a mulkinsa karo na farko.

"Obasanjo ya ce Buhari ba zai ci zabe karo na biyu ba, amma Buharin ba ci zabe ba? Dama ba na ce Obasanjo zai sha kunya ba lokacin da za a fadi sakamakon zabe.

"Nasarar shugaban kasa ya nuna cewa Allah ne kadai ke bayar da mulki kuma babu wani mutum da zai ce shine zai fadi abinda za ayi a kasar nan," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel