Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina

Yan bindiga a daren ranar Talata, 14 ga watan Mayu sun kashe mutum 20 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina.

Kauyukan da abun ya shafa sun hada da Dan Marke Z, Dan Sabau da kuma Karya wadanda ke raba iyaka da jihar Zamfara.

Shugaban kwamitin mika mulki na yankin, Anas Isa, ya tabbatar da lamarin a jiya Laraba, 15 ga watan Mayu.

Yace yan bindigan sun zo sannan suka bude wuta akan mazauna yankin kafin suyi masu fashin wasu daga cikin dabbobinsu.

Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina
Source: UGC

Ya bayyana hare-haren a matsayin abun bakin ciki “mussamman a wannan wata mai tsarki.

“Mun gudanar da taron tsaro inda muka yanke shawarar samun gwamnatin jihar domin ci gaba da sanar dasu akan lamarin.

“Abun shine kawai aje a shiga wannan daji sannan a tunkare su gaba da gaba, shine mafita.

KU KARANTA KUMA: Rashin Imani ruwa ruwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya yar wata 3 a Duniya

“Yan bindigan sun fi jami’an tsaron da ke kasa yawa sannan kuma kasancewar yankin mai duwatsu da hanyoyi marasa kyau, kafin hukumomin tsaro su isa gare su, sun kammala ayyukansu, don haka kawai kamata yayi aje a fuskance su."

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah yace rundunar zata yi bincike akan lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel