Rashin Imani ruwa ruwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya yar wata 3 a Duniya

Rashin Imani ruwa ruwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya yar wata 3 a Duniya

Wasu gungun yan bindiga sun kai mummunar farmaki a kauyen Kanoma dake cikin karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara inda suka kashe mutane biyu, tare da yin awon gaba da wasu mutane bakwai, daga ciki har da mai jego da jaririyar da take shayarwa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani mazaunin kauyen, mai suna Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa daruruwan yan bindiga ne suka diran ma kauyensu akan babura dauke da muggan makamai da misalin karfe 3 na daren Talata.

KU KARANTA: Makashinka yana tare da kai: Atiku na cin dunduniyar gwamnatin Buhari – Lai Muhammad

“Shigowarsu keda wuya suka shiga harbin mai kan uwa da wabi, inda suka bindige wasu mutane biyu da suka fice daga gidajensu saboda tsananin rudewa, mun yi kokarin kiran jami’an tsaro dake kan hanyar Gusau zuwa Sokoto domin su kawo mana dauki amma babu hali.

“Kai tsaye suka wuce gidan wani dan kasuwa mai suna Dan Hajia, inda suka daddakeshi da karfen rodi, suka raunatashi, sa’annan suka yi awon gaba da matarsa mai jego tare da yar jaririyar da take shayarwa mai watanni uku kacal a duniya.

“Sa’annan suka garzaya gidan wani tsohon jami’in gwamnati, Sani Abdullahi, inda suka tafi dashi tare da wasu mutane guda shida da bamu san inda suke ba har yanzu, daga bisani sun tuntubi iyalan wadanda suka sace suna neman naira miliyan 50 kudin fansa.” Inji shi.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar Zamfara, kaakain rundunar, Muhammad Shehu ya tabbatar da kai harin da kuma satar mutane 8, amma yace bashi da masaniya game da kisan wani ko wata a yayin harin.

Daga karshe yace tuni sun aika da kwararrun jami’an Yansanda domin su gudanar da bincike tare da bin sawun yan bindiga zuwa duk inda suka shiga don ceto mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel