Babba a Gwamnati ya bada makudan kudi a gyara gidan wani Mai gadi a Jigawa

Babba a Gwamnati ya bada makudan kudi a gyara gidan wani Mai gadi a Jigawa

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Boss Mustapha ya bada kyautar kudi har N500, 000 ga wani Mai gadi mai suna Musa Usman a jihar Jigawa. Sunan Malam Musa Usman yayi yawo a ko ina a Najeriya a cikin kwanakin nan.

An rahoto cewa wannan Bawan Allah yayi watsi da kyautar gida da aka yi masa, inda ya nemi a gidawa al’ummarsa rijiyar burtsatsai a madadin gida. Wannnan Bawan Allah yana aiki da wani kamfani ne a kasar, kuma ya isa ya ajiye aiki.

Musa Usman yana aiki ne a kamfanin wani mutumin kasar Indiya, Mista Varkey Verghese, da ke Legas. An yi ta rade-radin cewa Varkey Verghese ya nemi ya ginawa wannan mutumi gida a Kauyensa amma yace sam ba ya da bukata.

KU KARANTA: Wasu Mata 4 sun rasu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a Jigawa

Wannan mutumi yana ganin cewa idan har aka gina masa gida, shi da Iyalinsa ne kurum za su amfana, don haka ya nemi a gina rijiya inda kowa zai samu ruwa a garin. Wannan abu ya jawo masa lambar yabo daga ko ina a Najeriya.

Yanzu dai jama’a sun fara hadawa wannan mutumi kudi domin a gyara gidan sa, a kuma yi masa kwaskwarima da gyare-gyare. Verghese yace Boss Mustapha wanda shi ne SGF na wannan gwamnati ya fara da bada kudi N500, 000.

KU KARANTA: Yadda zaben 2019 ya kasance a Jigawa da wasu Jihohi

Sakataren gwamnatin kasar, Mustapha, ya jefa wannan makukun kudi ne jiya Laraba 15 ga Watan Mayu a cikin asusun da aka bude a banki na #Shellter4MusaUsmanCampaign da nufin gyara gidan wannan tsohon Mai gadi watau Musa Usman.

Kungiyar nan ta Water, Sanitation and Hygiene Media Network (WASH Media Network) ita ce ta shirya wannan gidauniyar taimako ga wannan mutumi, wanda aka yi masa shaida a wurin aiki wajen gaskiya da rikon amana a tsawon shekarun da yayi.

Ana zuba wannan kudi ne a cikin akawun din Shelter 4Musa Usman Campaign mai lamba na 203415584 a First Bank. Wani babban ma’aikacin kunigyar ta WASH Media Network yace ginin gidan da za ayi wannan mutumi yana da fa’ida sosai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel