Zargin juyin mulki: Makaryacin banza – Atiku ga Minista Lai Muhammad

Zargin juyin mulki: Makaryacin banza – Atiku ga Minista Lai Muhammad

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta zargin da gwamnatin Najeriya ta yi masa na cewa wai yana cin dunduniyar gwamnati, sa’annan ya bayyana Minista Lai Muhammed a matsayin makaryaci.

Legit.ng ta ruwaito gwamnatin tarayya ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar shugaban kasanta a zaben shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar da cin dunduniyar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yi musu bita da kulli.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya bayyana rashin jin dadinsa da sake nada shugaban babban banki

Sai dai a martanin daya mayar, Atiku yace “Bamu yi mamakin jin wadannan zarge zarge daga bakin Ministan Buhari, Lai Muhammed ba, don haka muna son jin dalilin da yasa gwamnatin Buhari ke kokarin makala ma PDP da dan takararta wannan jita jita ba.”

Atiku ya mayar da martani ne ta bakin kaakakinsa, Mista Paul Ibe, wanda yace Lai Muhammed yayi kaurin suna wajen furta kalaman karairayi, wanda har ta kai ga mataimakin shugaban kasa Osinbajo yana cewa bai dalilin da yasa Lai Muhammed bai sauya hali a lokacin Ramadan ba.

“Idan har wadanda suka dauki Lai Muhammed aiki suna tsoron karyarsa har a wata mai alfarma, watan Ramadana, toh mai zai sa yan Najeriya suyi mamakin irin wannan karya data fito daga bakinsa? Ta yaya mutanen da suka yi alwashin yin kare jini biri jini zasu zargi cikakken dan dimukradiyya da juyin mulki?” Inji shi.

Kaakakin ya soka ma Buhari magana inda yace Buhari ya taba yi ma zababbiyar gwamnatin dimukradiyya juyin mulki, sa’annan ya cigaba da tsanar mutumin da yayi ma juyin mulkin har bayan rasuwarsa, amma yace kowa ya san Atiku mutum ne mai son zaman lafiya, wanda bait aba wulakanta dimukradiyya ba.

Daga karshe kaakaki Ibe ya bayyana cewa Atiku na daya daga cikin jiga jigan tubalin da siyasar Najeriya da suka sha gwagwarmaya da fadi tashi wajen tabbatar da mulkin farar hula a Najeriya, sa’annan ya shawarci Lai daya koma ya fuskanci zargin badakalar da ake masana satar makudan kudade a ma’aikatar watsa labaru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel