Shugabannin APC su na neman jefa ni da Iyali na a hannun EFCC - Okorocha

Shugabannin APC su na neman jefa ni da Iyali na a hannun EFCC - Okorocha

Mun ji cewa mai girma gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya zargi shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da kuma wasu manyan jam’iyyar da jefa sa a hannun hukumar EFCC.

Gwamnan na Imo yana zargin shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da maka shi a wajen hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa domin a taso sa a gaba da bincike har a kama sa kuma a tsare shi.

Rochas Okorocha yake cewa an kai kararsa a kan wasu laifuffuka har 2 a gaban wani kotu da ke Abuja da nufin ayi ram da shi. Gwamnan yake cewa wasu manyan APC ne su ke son ganin ya kare a hannun EFCC idan ya bar ofis.

Kawo yanzu, gwamnan yace ya samu gayyata fiye da 25 daga wajen hukumomin da ke binciken sata da cin hanci a Najeriya da nufin kurum a bankado wani laifi da yayi wajen bada kwangiloli a jihar Imo, saboda a rufe sa a mari.

KU KARANTA: Mutanen Katsina sun koka da rashin tsaro sun yi fata-fata da allolin APC

Babban gwamnan na APC yace zagon-kasar da mutanen jam’iyyarsa ta APC su ke yi masa bai tsaya nan ba, domin kuwa har ta kai ana bin Iyali da Aminan sa da kulli. Gwamnan yace ba komai bane wannan illa neman hana sa sakat.

Daga cikin na-kusa da gwamnan da ake neman ganin bayansu akwai Aminan gwamnan da Surukunsa da Abokan siyasarsa irin su Uloma Rochas, Uju Rochas, Uchechi Rochas, Ahamefula Rochas, Amen Rochas, inji mai girma gwamnan.

Haka zalika gwamnan yace an taso Amamchi Rochas, Uzoma Anwukah da Uche Nwosu a gaba da bincike iri-iri saboda a same su da laifi. Gwamnan yake cewa bai aikata ba-daidai ba don haka ya nemi kotu tace EFCC ta shafa masa lafiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel