Majalisar dattijai ta wanke babban gwamnan CBN daga zargin badakalar N500bn

Majalisar dattijai ta wanke babban gwamnan CBN daga zargin badakalar N500bn

Kwamitin majalisar dattijai a kan bankuna, inshora, da ragowar harkokin da suka shafi kudi ya wanke babban gwamnan bankin kasa (CBN) daga zargin badakalar biliyan N500.

Emefiele na jiran majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin gwamnan CBN a karo na biyu bayan shugaba Buhari ya sake aika sunan sa domin neman sahalewar majalisar.

Bayan shugaba Buhari ya aike da sunan Emefiele majalisar ne aka samu bayyanar wani sautin murya da aka nada, wanda a cikin sa ake zargin Emefiele da wasu hadiman gwamnati na tattauna yadda zasu waske da biliyan N500 daga CBN zuwa wasu asusu na kasuwanci.

Da Emefieleya bayyana a gaban kwamitin ranar Laraba domin tantance shi, sai shugaban kwamitin na majalisar dattijai, Rabiu Ibrahim, ya yi watsi da zargin da ake yiwa Emefiele tare da bayyana cewar: "su na son cin dunduniyar ka ne saboda kai mutumin kirki ne."

Majalisar dattijai ta wanke babban gwamnan CBN daga zargin badakalar N500bn

Godwin Emefiele
Source: Depositphotos

Sannan ya cigaba da cewa: "ba ni da wata tambaya da zan yiwa gwamnan CBN. Na gama gamsuwa da nagartar sa. Ina yi maka fatan alheri da yi maka addu'ar Allah ya cigaba da kare ka.

DUBA WANNAN: Jakadan Saudiyya ya sha ruwa tare da hadimar Buhari, Abike Dabiri

"Yanzu mun san dalilin da yasa ake maka bita da kulli. Haka wasu 'yan Najeriya yanzu ke kirkirar bidiyo da sharri kala-kala domin bata sunan duk wani mutum mai mutunci.

"Ba zamu bata lokaci ba wajen mika rahoton mu a gaban majalisa ba domin a tabbatar da kai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel