PDP na kokarin hambarar da gwamnatin Buhari – Gwamnatin tarayya

PDP na kokarin hambarar da gwamnatin Buhari – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa, Atiku Abubakar da kokarin kulla wa gwamnatin shgaban kasa Muhammadu Buhari wani makirci.

Gwamnatin Buhari ta ja kunnen PDP da dan takarar nata kan cewa su sake takunsu ko kuma su fuskanci tuhuwa akan yiwa kasar zagon kasa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, 15 ga watan Mayu a fadar Shugaban kasa.

A cewar Lai, ba daidai bane hukuncin da PDP da Atiku suke yunkurin dauka, inda yace maimakon su rungumi kaddara bayan da suka fadi a zabe, sai suke so su yi amfani da wannan damar wajen yi wa gwamnati zagon kasa.

PDP na kokarin hambarar da gwamnatin Buhari – Gwamnatin tarayya

PDP na kokarin hambarar da gwamnatin Buhari – Gwamnatin tarayya
Source: Facebook

Ministan ya zarge PDP da dan takarar ta da furta wasu kalamai da suka fi kama da yi wa kasa bita-da-kulli, inda ya bada misalin wata magana da Atiku ya ta furta, cewa; in har ‘yan Najeriya ba su yaki APC ba, to kashe-kashe ba zai yi sauki ba a kasar.

KU KARANTA KUMA: Tinubu yana neman sa-hannun ‘Yan Majalisa a kan canza Ranar Damukaradiyya

“Gwamnatin tarayya na Allah-wadai da ayyukan da wasu marasa kishin kasa ke yi, musamman ma dai abinda jam’iyyar PDP ke yi, akwai hatsari in har ba a tsayar da wannan lamarin ba, don haka muke gargadinsu,” inji Lai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel