Bayin Allah sun yi zanga-zanga a kan yawan kashe-kashe a Batsari

Bayin Allah sun yi zanga-zanga a kan yawan kashe-kashe a Batsari

Jama’an da ke zama a cikin karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina, sun fita gari sun shirya zanga-zanga domin nuna rashin jin dadinsu a kan yawan kashe-kashen da ake fama da shi a cikin jihar.

Kamar yadda mu ka samu labari a cikin makon nan daga jaridar Niger Watch, Mutanen Garin na Batsari sun fito sun yi raga-raga da allolin yakin neman zaben jam’iyyar APC na Shugaban kasa Buhari da kuma Gwamna Aminu Bello Masari.

Masu zangar-zangar wanda su ka hada da manyan maza da ‘yan mata da kuma kananan yara sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina da kuma jami’an tsaro su kara kokarin ganin sun kare rayukan al’umma da ke yankin.

Rahoton ya bayyana cewa wadanda su ka fusata sun rika kona tayoyi, sannan kuma su ka rusa hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai girma gwamna Aminu Bello Masari domin nuna fushinsu a kan halin dar-dar din da ake ciki.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: Mu na bakin kokarin mu - Buhari

Kashe-kashen al’umma dai yayi kamari musamman a cikin Garin Batsari da kuma wasu kananan hukumomi kusan 8 a jihar ta Katsina inda nan ne Mahaifar shugaban kasa. Wannan ya jawo wannan zanga-zana a Ranar Talatan nan.

A wancan makon dai an kashe mutane a wani Kauye da ake kira Wagini a Garin na Batsari. ‘Yan bindiga ne su ka shigo cikin mutane, su ka shiga buda wuta har ta kai aka rasa dinbin dukiya da rayukan al’ummar da ba su ji, ba su sha ba.

Yanzu dai wasu da-dama su na ta faman barin Garin na Batsari a Ranar Talata 14 ga Watan Mayu bayan da wasu jami’an tsaro na ‘Yan sakai su ka kashe wani kasurgumin ‘dan bindiga da ya gagara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel