Abinda na ke son jama'an Bauchi su tuna ni da shi - Gwamna Abubakar

Abinda na ke son jama'an Bauchi su tuna ni da shi - Gwamna Abubakar

Gwamnan Bauchi mai barin gado, Mohammed Abubakar ya ce yana son jama'an Bauchi su tuna da shi a matsayin wanda ya kawo tsari da zaman lafiya a siyasar jihar.

Abubakar dai ya sha kaye ne wurin tsohon minisatan babban birnin tarayya, Abuja, Bala Mohammed a babban zaben shekarar 2019.

A jawabin da ya yi bayan ganawa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce yana son a tuna da shi a matsayin wanda ya kawo zaman lafiya a jihar Bauchi.

Abinda na ke son Jam'an Bauchi su tuna ni da shi - Gwamna Abubakar

Abinda na ke son Jam'an Bauchi su tuna ni da shi - Gwamna Abubakar
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

"Idan za ka iya tunawa jihar Bauchi yana daya daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikice. Tun lokacin da muka karba mulki zuwa yanzu, munyi nasarar tabbatar da zaman lafiya.

"Baya ga zaman lafiya munyi nasarar kawo cigaba sosai a fanin zaman lafiya, ilimi da ayyukan cigaba. Saboda haka ina son mutane su tuna da ni a matsayin wanda ya kawo zaman lafiya a jihar," inji shi.

Ya bukaci mutanen jihar su cigaba da zama lafiya tare da junansu tare da biyaya da dokoki da hukuma kamar yadda aka san su.

A kan dalilin ziyarsa wurin mataimakin shugaban kasar, ya ce, "Na zo kawo masa ziyara ce domin tattaunawa kan wasu al'amura kamar yadda muka saba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel