An bankado yunkurin kai wa matatun man fetur hari

An bankado yunkurin kai wa matatun man fetur hari

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta gani wata makirci da wasu azzalumai suka shirya na niyyar kai hari a wasu matatun man fetur a Najeriya.

A cewar sanarwar da Kakakin 'yan sanda, Frank Mba ya fitar a ranar Laraba, miyagun mutanen suna basaja a matsayin masu fafutikan kare muhalli da dumamar yanayi ne.

"Sunyi shirin kai muggan hare-hare a matatun man fetur na sassan Najeriya musamman a yankin Neja-Delta da jihohin da ke makwabtaka da su," inji Mba.

'Yan sandan sun ce wannan harin yana da nasaba da siyasa.

An bankado yunkurin kai wa matatun man fetur hari

An bankado yunkurin kai wa matatun man fetur hari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

"Sunyi niyyar lalata matatun man fetur. Suna son su kawo cikas ga tsaron kasa da tattalin arzikin kasar musamman abinda ya shafi kasuwar duniya na man fetur.

"Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya umurci kwamishinonin 'yan sanda a jihohin da akayi niyyar kai hare-haren su tsananta tsaro a matatun man fetur da sauran manyan hukumomin kasa.

"An bukaci kwamishinonin 'yan sanda da sauran kwamandoji su dauki matakin kiyaye afkuwar harin. An dauki wannan matakan ne domin kare harin da kuma damke wadanda suka shirya wannan makircin," inji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel