Tinubu yana neman sa-hannun ‘Yan Majalisa a kan canza Ranar Damukaradiyya

Tinubu yana neman sa-hannun ‘Yan Majalisa a kan canza Ranar Damukaradiyya

Babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, yayi kira ga ‘yan majalisar tarayya na kasar nan da su yi wa dokar Ranar damukaradiyya garambawul.

Jigon na APC yana so majalisa tayi wa dokar kasa garambawul domin a tabbatar da Ranar 12 ga Watan Yuni a matsayin Ranar Damukaradiyya a Najeriya, bayan shugaban kasar ya sa hannu a rika tunawa da wannan babba Rana a fadin Najeriya.

Bola Tinubu yake cewa shugaba Buhari yayi abin da ya dace na maida 12 ga Watan Yuni ta zama Ranar Damukaradiyya. Jagoran na APC yayi wannan jawabi ne bayan Ministan labarai na kasar Lai Mohammed ya fito yayi magana jiya.

KU KARANTA: Buhari zai sake karbo wani danyen bashi daga Kasar waje

Ministan ya bayyana cewa duk da cewa za a rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a Ranar 29 ga Watan Mayu, za a yi kananan bukukuwan da aka shirya domin tunawa da damukaradiyya ne daga baya a Ranar 12 ga Yuni.

Tsohon gwamnan na Legas yayi jawabi ne ta bakin babban Hadiminsa, Tunde Rahman. Tinubu yake cewa akwai bukatar a yabawa matakin da Buhari ya dauka na tunawa da Watan Yuni sannan kuma yayi wa dokar kasa biyayya.

Tinibu yace Buhari yayi wa doka biyayya da za a sake rantsar da shi a cikin wannan Watan ganin cewa har yanzu ba a karkare yi wa kundin tsarin mulki garambawul din za ta bada dama a rika rantsar da masu mulki a Watan Yuni ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel