Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade

Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade

-Jam'iyar adawa ta PDP ta bukaci Buhari yayi bincike akan N14trn da sukayi sama ko kasa tsakanin ma'aikatar man fetur da kuma NNPC

-A cewar PDP, rashin yin wannan bincike zai tabbatar mana da cewa akwai abinda shugaban kasan yake boyewa

Jam’iyar adawa ta PDP ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari kwanaki 14 na ya gudanar da bincike akan kudade da sukayi sama ko kasa karkashin kamfanin mai na kasa wato NNPC. Kudin da ake neman yawansu yakai N14trn a cewar PDP.

Jam’iyar ta PDP ta nemi shugaba Buhari ya binciki makomar wadannan kudade kafin ranar 29 ga watan Mayu, 2019 wacce itace ranar da wa’adinsa na farko a kan mulki zai kare. A cewar jam’iyar idan har da gaske wannan gwamnati keyi cewa tana yaki da cin hanci to lallai ta nemo wadannan kudade.

Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade

Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade
Source: UGC

KU KARANTA:‘Yan siyasa na da hannu cikin tabarbarewar tsaro a Arewa, inji Buratai

Jam’iyar adawan tayi kira ga hadimin shugaban kasa mai bada shawara akan lamuran da suka shafi cin hanci, Farfesa Itse Sagay na ya taimakawa shugaban kasa wurin gudanar da wannan bincike.

A wani zance da ya fito daga hannun sakataren hulda da jama’a na jam’iyar PDP, Kola Ologbondiyan, ikirari yayi cewa “ gwamnatin Buhari takai mutuka wajen cin hanci.”

A don haka jam’iyar PDP na rokon Buhari ya binciki makomar wadannan kudade wanda sukayi sama ko kasa tsakanin ma’aikatar man fetur da kuma kamfanin tatar mai na NNPC.

“ Sai dai kuma idan shugaban kasa yana boye wani abu ne game da kudin, amma indai ba haka yakamata ya dauki matakin yin bincike cikin kwanaki 14.” A cewar zancen nasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel