Gwamnatin Najeriya za ta ci bashin Dalar Amurka Biliyan 1 daga kasar Sin - Majalisar Zantarwa

Gwamnatin Najeriya za ta ci bashin Dalar Amurka Biliyan 1 daga kasar Sin - Majalisar Zantarwa

Majalisar zantarwa yayin zamanta na ranar Laraba, 15 ga watan Mayun 2019, ta bayar da lamunin sake karbar bashin dalar amurka biliyan daya daga kasar Sin.

Rahotanni kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito sun bayyana cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu lamunin majalisar zantarwa na karbar bashin dalar Amurka biliyan daya daga kasar Sin domin aiwatar da aikin samar da wutar lantarki.

Shugaban kasa Buhari yayin jagorantar zaman majalisar zantarwa a fadar Villa

Shugaban kasa Buhari yayin jagorantar zaman majalisar zantarwa a fadar Villa
Source: Facebook

Kasar Najeriya za ta karbi bashin ta hanyar bankin China-Exim na kasar Sin domin aiwatar da katafaren aikin tashar Gurara ta biyu domin samar da wutar lantarki wato Gurara II hydro project.

Kamar yadda ake kyautata zato da tsammani, ana sa ran katafaren aikin zai samar da nauyin megawatts 360 na wutar lantarki a kasar nan.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun hallaka sojoji 17 a harin kwanton bauna

Ministan ruwa na kasa Mista Sulaiman Aliyu, shi ne ya bayar da shaidar wannan lamuni da majalisar zantarwa tayi na karbar bashi domin inganta ci gaban kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zantarwa a ranar Laraba da aka gudanar cikin fadar sa ta Villa dake babban birni na tarayya Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel