Gudaji Kazaure ya bayyana rashin jin dadinsa da sake nada shugaban babban banki

Gudaji Kazaure ya bayyana rashin jin dadinsa da sake nada shugaban babban banki

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni da yan Kwashi, Muhammad Gudaji Kazaure yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da canza ra’ayinsa game da sake nada Godwin Emiefele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN.

Kazaure ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, inda yace akwai kwararrun mutanen da suka fi kamata su rike wannan kujera ta gwamnan bankin Najeriya.

KU KARANTA: Za’a kashe N4,068,000,000 wajen tarbar zababbun yan majalisun dokokin Najeriya 469

Gudaji Kazaure ya bayyana rashin jin dadinsa da sake nada shugaban babban banki

Emiefele da Gudaji
Source: UGC

Legit.ng ta ruwaito a makon data gabata ne shugaba Buhari ya aika ma majalisar dattawan Najeriya da bukatar tantance Emiefele domin duba cancantarsa ta sake zama shugaban babban bankin Najeriya a karo na biyu.

Sai dai Gudaji Kazaure ya bayyana cewa kungiyon goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka hada da Buhari Support Group, Buhari Campaign Organisation da kuma Buhari Die Hard Group basu ji dadin wannan mataki da Buhari ya dauka ba.

A cewar Gudaji, Emiefele bai tabuka wani abin azo a gani ba a zamansa a matsayin shugaban CBN ba, musamman idan aka yi duba ga yadda darajar naira ta fadi warwas daga naira 180 zuwa naira 360.

“Haka zalika Emiefele na daga cikin kusoshin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, gwamnatin da tayi kaurin suna wajen handama da babakere, kuma duk Emiefele na kallo aka tafka wadannan barna bai ce uffan ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel