Jakadan Saudiyya ya sha ruwa tare da hadimar Buhari, Abike Dabiri

Jakadan Saudiyya ya sha ruwa tare da hadimar Buhari, Abike Dabiri

Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Adnan Mahmoud Bostaji, ya karbi bakuncin shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya dake zaune a kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa; ministan Abuja, Muhammad Bello; ministan yada labarai, Lai Mohammed, da sauran wasu manya a gwamnatin Najeriya, inda suka sha ruwa tare a Abuja.

Ambasadan ya karbi bakuncin wasu 'yan Najeriya domin shan ruwa tare a gidan jakadancin kasar Saudiyya dake Dunes a Abuja.

"Irin wannan taro yana da muhimmanci ga dangantakar dake tsakanin kasar Saudiyya da Najeriya. Halartar manyan jami'an gwamnatin Najeriya ya nuna irin abota da kaunar dake tsakanin kasashen biyu," a cewar Bostaji.

Jakadan Saudiyya ya sha ruwa tare da hadimar Buhari, Abike Dabiri
Jakadan Saudiyya da Abike Dabiri
Asali: Twitter

Jakadan Saudiyya ya sha ruwa tare da hadimar Buhari, Abike Dabiri
Jakadan Saudiyya da ministan Abuja
Asali: Twitter

Bostaji ya bayyana cewar tun shekarar 1960 Najeriya da kasar Saudiyya suka kulla alaka mai karfi, wacce ya ce yana da yakinin cewar za ta cigaba da dorewa.

Liyafar shan ruwan da Bostaji ya shirya a ranar Talata ta samu halartar wakilin kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) a Najeriya, Ambasada Babatunde A. Nuredeem; jakadn kasar Koriya, Lee In Tae da jakadan kasar Bangladesh a Najeriya, Shameem Ahsan da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel