Al-Makura ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Nasarawa

Al-Makura ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Nasarawa

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa ya sallami dukkan masu rike da mukamman siyasa a jihar gabanin karewar wa'adinsa a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayu.

Al-Makura ya sanar da sallamar masu rike da mukaman siyasar ne yayin taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a ranar Laraba a Lafia babban birnin jihar.

Ya ce ya dauki matakin ne domin saukaka mika mulki zuwa ga zababen gwamnan jihar Mr Abdullahi Sule.

Al-Makura ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Nasarawa

Al-Makura ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Nasarawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Sai dai Al-Makura ya ce wasu daga cikin jami'an gwamnatin na sa masu rike da muhimman makamai za su cigaba da ayyukansu har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Ya kuma umurci dukkan kwamishinoninsa su tattara rahotanninsu na aiki su mika masa kafin ranar 20 ga watan Mayu.

Gwamnan ya ce rahotannin za su taimakawa wadanda za su gaje su.

Ya ce bayan sun mika rahotannin ayyukansu dukkan kwamishinonin za su cigaba da kasancewa a ofisoshinsu har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

"Tare muka zo kuma tare za mu tafi.

"Za muyi aiki tukuru domin tabbatar da cewa mun mika mulki ga gwamnati mai zuwa ba tare da cikas ba," inji Al-Makura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https//facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel