Gobarar titi: Ganduje ya bawa Zainab kyautar miliyan uki

Gobarar titi: Ganduje ya bawa Zainab kyautar miliyan uki

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bawa matashiyar nan Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar da hukumomin kasar Saudiyya suka saki daga gidan yari kyautar miliyan N6m; miliyan uku ga kowannen su.

Ganduje ya basu kyautar ne a yau bayan shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasashen ketare, Abike Dabiri, ta jagorance su zuwa wurin gwamnan a gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba.

Kakakin gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, ne ya bayyana da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya kara da cewa gwamna Ganduje ya mika godiya ga dukkan wadanda suka taka rawar gani, musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari, wajen ceto mutanen biyu.

Hukumomin Saudiyya sun kama Zainab da Ibrahim bisa zarginsu da shiga kasar da miyagun kwayoyi, amma daga baya aka sake su bayan gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani tare da tabbatar wa kasar Saudiyya cewar basu aikata laifin da ake zarginsu da shi ba.

Gobarar titi: Ganduje ya bawa Zainab kyautar miliyan uki

Zainab a gidan gwamnatin jihar Kano
Source: Twitter

A ranar Litinin ne Legit.ng ta kawo muku labarin cewar Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya bayan gwamnatin kasar Saudiyya ta sake ta.

DUBA WANNAN: Abinda yasa ragowar kabilun Najeriya ke yiwa 'yan kabilar Igbo mummunar fahimta - Rochas

An kama dalibar yar Najeriya a kasar Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi sannan daga bisani aka sake ta bayan gwamnatin Najeriya ta sanya baki a lamarin.

Zainab dai ta dawo gida ne ranar Litinin, 13 ga watan Mayu da misalin karfe 10:00 na safe. Jirgi ya sauke ta a Kano inda ta tarar da dandazon yan uwa da abokan arziki suna jira domin tarbar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel