Kakakin majalisar dokoki ya sace sandan majalisa a Imo don kada a tsige shi

Kakakin majalisar dokoki ya sace sandan majalisa a Imo don kada a tsige shi

'Yan majalisu 21 cikin 27 ne suka amince da tsige kakakin majalisar a yau Laraba.

An dakatar da Acho Ihim ne bayan ya dakatar da zaman majalisar sannan ya tsere da sandan ikon majalisar bayan ya karonto wasikar dage dakatarwar da aka yiwa shugabanin kananan hukumomi 27 a jihar da majalisar da dakatar a makon da ya gabata.

Punch ta ruwaito cewa Ihim ya yi kokarin hana a tsige shi inda ya umuri hadimansa su kashe janareta da ke bawa majalisar wutan lantarki amma duk da hakan 'yan majalisar sun cigaba da zamansu duk da ransu ya baci.

Kakakin majalisar dokokin Imo ya yi batar dabo da sandan ikon

Kakakin majalisar dokokin Imo ya yi batar dabo da sandan ikon
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Rikici ya barke ne yayin da 'yan majalisar suka nuna kin amincewarsu da wasikar soke dakatarwar da aka yiwa shugabanin kananan hukumomin 27.

Wani dan majalisa ya bukaci a bashi damar tofa albarkacin bakinsa a kan batun amma Kakakin majalisar bai bashi damar ba kawai ya amince da sakon da ke cikin wasikar.

Rahotanni sun bayyana 'yan majalisar suna kammala shirye-shiryen tsige kakakin majalisar ne a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel