Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu

Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu

- A karon farko shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yaba da wani aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kasar nan

- Ya yaba mishi akan hanyar da yabi ta diflomasiyya wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu wacce kasar Saudiyya ta kama da zargin shiga da kwaya kasar

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yaba da kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta fannin diflomasiyya wurin ganin an sako Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar daga gidan yarin kasar Saudiyya, bisa zargin da ake musu na shiga da miyagun kwayoyi kasar.

Mista Saraki, wanda ya yi yabon na shi a lokacin da Sanata Kabiru Gaya ya ta so da zancen a majalisa ranar Talata, ya ce sakin su ba karamin sauki ba ne ga 'yan Najeriya.

Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu

Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu
Source: UGC

Zainab Aliyu wacce ta ke daliba ce a Jami'ar Maitama Sule, da ke Kano, da kuma Ibrahim Abubakar, an kama su ne a kasar Saudiyya, bisa zargin shiga kasar da miyagun kwayoyi, inda aka kamata a filin tashi da saukar jiragen sama na Prince Mohammed Bin Abdulaziz da ke Madina, saboda an gano kwayar a cikin jakarta.

Zainab, ta yi yunkurin kare kanta, inda ta bayyana cewa saka mata kwayar aka yi a cikin jakarta.

Bugu da kari, an kama Abubakar shi ma a kasar da laifin shiga da kwaya.

KU KARANTA: Kano: Wani mutumi ya yiwa wata budurwa yankan rago saboda ta ki bashi hadin kai

Yayin da yake magana akan doka ta 43 ta majalisar dattijai, Mista Gaya ya ce ya kamata a yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Majalisar Dattijai, da duk wadanda suka ba da gudummawa wajen sakin su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Sakataren Ma'aikatar Harkokin Waje, Mustapha Sulaiman, wanda ya tabbatar da sakin su, ya ce an sake sune sakamakon an bi hanya ta diflomasiyya tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel