'Yan Bindiga sun hallaka sojoji 17 a harin kwanton bauna

'Yan Bindiga sun hallaka sojoji 17 a harin kwanton bauna

Mun samu cewa wani mummunan harin kwanton bauna a ranar Larabar da ta gabata ya salwantar da rayukan dakarun sojin kasar Nijar 17 a kan iyaka ta gabar kasar Mali yayin aka nemi 11 aka rasa bayan kwana guda da aukuwar harin.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, harin ya auku ne a ranar Talatar da ta gabata daura da kauyen Tongo dake yankin Yammacin Tillaberi a kasar dake makotaka da kasar Najeriya wato Nijar.

'Yan Bindiga sun hallaka sojoji 17 a harin kwanton bauna

'Yan Bindiga sun hallaka sojoji 17 a harin kwanton bauna
Source: Twitter

Rahotanni daga kafar watsa labarai ta jaridar AFP ta bayyana cewa, yankin na garin Tillaberi ya yi daidai da inda wani mummunan hari na kwanton bauna ya salwantar da rayukan dakarun sojin kasar Amurka hudu da kuma na kasar Nijar a shekarar 2017 da ta gabata.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya ba Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar kyautar miliyan uku-uku

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, 'yan bindiga sun hallaka dakarun sojin kasar Mali 17 tare da raunata kimanin 34 yayin mummunan hari da ya auku a sansanin dakaru dake yankin kasar Mali ta tsakiya a shekarar 2016.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel