Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Manyan 'yan jihar Kano karkashin kungiyar 'Abokan Demokradiyya' sun bayyana damuwarsu a kan rikicin da ke faruwa a jihar Kano bayan kirkiran sabbin masarautu hudu da gwamnatin jihar tayi.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kirkiri sabbin masarautu da sarakuna masu daraja ta farko wadda wasu ke zargin anyi hakan ne domin rage karfin mulkin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Bashir Tofa, Dokta Usman Bugaje, Dakta Abubakar Siddique Mohammed, Bashir Yusuf Ibrahim, Bilya Bala, Hubert Shaiyen da Farfesa. Jibrin Ibrahim, kungiyar tayi gargadin cewa kirkiran sabbin masarautan zai iya raba kan jama'a a jihar.

Kirkiran masarautun Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje sun cacaki Ganduje

Kirkiran masarautun Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje sun cacaki Ganduje
Source: Twitter

A cewarsu, kirkiran sabbin masarautun zai iya jefa siyasa a cikin masarautan jihar kuma akwai yiwuwar samun tashin hankali duba da cewa akwai mutane da yawa da basu goyon bayan kirkiran sabbin masarautun.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Kungiyar tayi kira ga Gwamna Abdullahi Ganduje ya sake bibiyar matakin da ya dauka kuma ya yi aiki tare da majalisar dokokin jihar da masu sarautun gargajiya da dattawan jihar.

Sun kuma bukaci majalisar jihar ta kira taron jin ra'ayin jama'a a kan batun domin tabbatar da zaman lafiya tare da kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen Gwamna Ganduje ya janye kirkiran masarautun.

"Ya kamata a sani cewa idan rikici ya barke a Kano, yana iya shafan yankin arewa ko kasar naki daya.

"Ran mutane ya baci kuma wasu za su iya amfani da wannan damar domin tayar da fitina.

"Gwamnatin tarayya, musamman shugaban kasa ya kamata ya yi gaggawar sanya baki a cikin lamarin," kamar yadda wata bangare na sanarwar ta ce.

Sanarwar ta cigaba da cewa, "muna matukar damuwa a kan rikicin da ke faruwa a Kano bayan kirkiran sabbin masarautu da gwamnatin jihar tayi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel