Buhari ya amsa gayyatar Saudiyya, zai tafi Umrah

Buhari ya amsa gayyatar Saudiyya, zai tafi Umrah

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiya a ranar Alhamis.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya ce Buhari zai tafi Saudiya ne domin amsa gayyatar da Sarkin Saudiya ya masa domin zuwa ya yi Umrah.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa gayyatar Sarki Salman Bin Abdulazeez, Sarkin Saudiya domin zuwa yin Umrah a kasar.

"Saboda haka, shugaban kasar zai tafi a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu tare da wasu mukarrbansa.

"Ana sa ran zai dawo Najeriya a ranar Talata 21 ga watan Mayu.

"Umrah ba farilla bane amma sunnah ce wadda akan tafi zuwa kasa mai tsarki domin yi a kowanne lokaci a cikin shekara," inji Garba Shehu.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

A baya-bayan nan ne Buhari ya dawo daga wata ziyarar kwanaki 10 da ya kai kasar Ingila. Har yanzu ba a bayyana dalilin kai ziyarar shugaban kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel