Jami’an DSS sun gayyaci wani shahararren malamin addinin Musulunci, sun kuma tsare shi a Katsina

Jami’an DSS sun gayyaci wani shahararren malamin addinin Musulunci, sun kuma tsare shi a Katsina

Jami’an rundunar yan sandan farin kaya sun gayyaci wani malamin addinin Musulunci mazaunin Katsina, Mallam Aminu Usman wanda aka fi sani da Abu Ammar, sannan sun tsare shi.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kamun Abu Ammar wanda aka yi a ranar Talata, 14 ga watan Mayu baya rasa nasaba da hudba da yayi, inda ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan dada haddasa rashin tsaro a fadin kasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abu Ammar na tare da abokinsa, Malam Shamsu, lokacin da ya amsa kiran gayyata daga jami’an tsaro wanda suka nemi ya zo ofishin DSS da ke jihar.

Jami’an DSS sun gayyaci wani shahararren malamin addinin Musulunci, sun kuma tsare shi a Katsina
Jami’an DSS sun gayyaci wani shahararren malamin addinin Musulunci, sun kuma tsare shi a Katsina
Source: UGC

Yaron malamin, Murtala ya tabbatar da kamun nasa ga manema labarai a gidansa da ke yankin Filin Samj a ranar Laraba, 15 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace karo na farko kenan da yake jin labarin a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa kan lamarin.

Idan za a tuna a watan Maris 2015 hukumar DSS ta taba tafiya da Abu Ammar kan wani abu makamancin wannan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel