Kansila ya sha duka a hannun 'yan bangan siyasa a Edo

Kansila ya sha duka a hannun 'yan bangan siyasa a Edo

Hon. John Momoh, kansila mai wakiltan mazaba na tara a karamar hukumar Estako yana kwance a asibiti sakamakon duka da wasu 'yan bangan siyasa suka yi masa.

An garzaya da Momoh zuwa asibitin kwararru na gwamnati da ke karamar hukumar Esan ta Tsakiya ne inda aka farfado da shi sannan aka saka masa na'urar nimfashi.

The Nation ta ruwaito cewa wadanda ake zargi 'yan daba ne sun kai farmaki sakatariyar garin Fugar inda kansilolin ke tattaunawa kuma suka rufe Momoh da wasu kansiloli biyu da duka; Hon Kadiri Roger da Prince Dauda Anakhu Amedu.

Kansila ya sha duka a hannun 'yan daba yayin da suka kai masa hari
Kansila ya sha duka a hannun 'yan daba yayin da suka kai masa hari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Daga bisani an dakatar da kansilolin uku na watanni uku ba tare da albashi ba saboda rashin da'a ga doka da yiwa sauran abokan aikinsu barazana da makamai da kuma karya sandan ikon majalisa.

Sai dai Prince Amedu ya ce shugabanin kansilolin karamar hukumar ne ya shirya harin saboda yana ganin kansilolin uku ba su masa biyaya.

Amedu ya ce shugaban kansilolin ya ki bayar da motar daukan marasa lafiya domin a kai Momoh zuwa asibiti.

Ya ce suna korafi saboda rashin biyansu wasu allawus dinsu.

"Zan tafi kotu saboda babu wanda zai iya dakatar da kansila na fiye da watanni biyu. Za mu karbi kudaden mu."

Shugaban kansilolin Akhigbe ya ce bashi da hannu cikin harin da ake kaiwa kansilolin uku yayin zaman majalisar su.

Akhigbe ya ce majalisar ta cimma matsayar hana su allawus dinsu ne a maimakon dakatar da su.

Ya ce, "Bana Fugar a ranar da abin ya faru. Bani da 'yan daba. Kansilolin uku suna korafi ne saboda an hana su allawus dinsu N100,000 kowannensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel