INEC ta kwace takaidar shaidar cin zabe daga hannun Kawu Sumaila

INEC ta kwace takaidar shaidar cin zabe daga hannun Kawu Sumaila

A yayin da Hausawa ke yiwa ire-iren wannan lamari da an ga samu kuma an ga rashi, mun samu cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta kwace takardar shaidar cin zabe daga hannun tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC a ranar Litinin da ta gabata, ta mallaka takardar shaidar cin zabe ga zababben dan majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Sumaila da Takai na jihar Kano, Shamsuddeen Dambazau.

Honarabul Kawu Sumaila

Honarabul Kawu Sumaila
Source: UGC

Shamsuddeen Dambazau wanda ya kasance 'da ga Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya samu shaidar nasarar zabe yayin da hukumar INEC ta kwace takardar shaidar daga hannun tsohon hadimin shugaban kasa akan al'amurran da suka shafi majalisar tarayya, Honarabul Kawu Sumaila.

A ranar 18 ga watan Afrilun da ta gabata, wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a jihar Kano, ta yi watsi da cancantar takarar Honarabul Sumaila a matsayin gwanin dan takara na jam'iyyar APC.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar AAC ta nemi a cafke gwamnan bankin Najeriya

Tufka da warwarar ta auku a yayn da kotun ta gamsu da korafin Shamsuddeen na cewar Honarabul Sumaila bai tsaya an dama da shi ba wajen takara yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar dan majalisar tarayya da zai wakilci kananan hukumomin Sumaila da kuma Takai.

Yayin gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Shamsuddeen Dambazau, kwamishinan hukumar INEC ta kasa Amina Zakari, ta ce hakan ya dace da daidai na hukunci da kuma umurnin da babbar kotun kasa ta gindaya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel