Ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu satar mutane – Dambazau

Ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu satar mutane – Dambazau

Gwamnatin tarayya ta jadadda cewar ana samun gagarumin nasara a yaki da migayun ayyukan da ake aikatawa a kasar musamman a fannin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau ne ya bayyana hakan a taron shugabannin rundunonin 'yan-sanda na kasashen yammacin Afirka da ake gudanarwa a babbar birnin tarayya Abuja.

Ya ce: "gwamnatin na aiki tukuru da hadin-kan wasu shugabanni wajen ganin ta shawo kan matsalolin tsaro musamman garkuwa da mutane domin neman kudin fansa."

Manufar taron wanda ya samu halartar jami'an hukumar 'yan sandan kasa da kasa ita ce duba kalubalan tsaro da yankin ke fuskanta da kuma yadda masu aikata laifi ke ketara iyakokin kasashen.

Ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu satar mutane – Dambazau

Ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu satar mutane – Dambazau
Source: Depositphotos

Dambazau ya ce a baya ba a san matsalar garkuwa da mutane ba, amma dai a halin yanzu an dukufa ana tuntubar juna da wasu shugabannin daban-daban na yankuna don gani an kamo bakin zaren wannan al'amari.

Ministan ya kara da cewa "ba wai an gaza ba ne ta wani fannin kawai dai ba rana guda ake gano bakin zaren ire-iren wadanan matsalolin ba."

KU KARANTA KUMA: Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Ya kuma ce yanzu idan aka kwatanta da baya kusan ana iya cewa an samu "saukin" matsalar tsaro musamman a kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Har ila yau ya kuma ce an kama mutane da dama da ke cikin wannan harka ta satar mutane a yankunan da dama kamar su Zamfara da sauransu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel