Jam'iyyar AAC ta nemi a cafke gwamnan bankin Najeriya

Jam'iyyar AAC ta nemi a cafke gwamnan bankin Najeriya

Jam'iyyar AAC African Action Congress, ta nemi a gaggauta tsige gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele tare da sakaya shi biyo bayan takaddamar zargin cewa an wawuri wasu kudi har Naira Biliyan 500 na masu hannu jari daga bankin.

CBN ya karyata cewa akwai wasu makudan kudi da suka bace daga asusun sa. Bankin ya musanta wannan zargi cikin lafazin kakakin sa, Isaac Okafor da cewar zargin da ake yi akan sama da fadi da Naira bilyan 500 daga asusun bankin ba ya da wata madogara ta gaskiya.

Emefiele tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa

Emefiele tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Source: Twitter

Jaridar Sahara Reporters ta fito da sautin murya na wata tattaunawa da aka yi tsakanin gwamnan babban bankin na kasa, Godwin Emefiele, mataimakin sa Edward Lametek Adamu da kuma wani mai ba gwamnan bankin shawara, Mista Emmanuel Ukeje.

Cikin faifan sautin daukan murya, an ji yadda Mista Emefiele yake bayani akan wasu makudan kudi na masu hannun jari da suka lalace a cikin bankin, inda ya yi furucin neman yadda za a fanshe daga baitul malin gwamnatin kasar nan.

KARANTA KUMA: Maki 370 na kudirta zan samu - Dalibin da ya fi kowa samun nasara a jarabawar JAMB ta bana

A sanadiyar wannan takaddama ta zargin zamba cikin aminci mai barazanar zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, jam'iyyar AAC cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin ta, Rachel Onamusi, ta nemi a gaggauta fatattaka tare dadume gwamnan bankin Najeriya da sauran ababen zargi.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a karshen makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tsawata wa'adin mukamin gwamnan bankin Najeriya tun yayin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi a shekarar 2014 da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel