Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tantance Emefiele bayan Buhari ya sake nada shi

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tantance Emefiele bayan Buhari ya sake nada shi

Godwin Emefiele wanda ya kasance gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan banki, inshora da sauran hukumomin kudi domin taantancewa.

A cewar jaridar Daily Trust, Emefiele ya gurfana domin tantancewa a ranar Laraba, 15 a watan Mayu.

Tantancewar na zuwa ne bayan umurnin da majalisar dattawa ta ba kwamitin.

Sanata Rafiu Ibrahim (PDP, Kwara) ne ke jagorantar kwamitin.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tantance Emefiele bayan Buhari ya sake nada shi

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tantance Emefiele bayan Buhari ya sake nada shi
Source: Twitter

Emefiele, wanda aka nada a matsayin gwamnan CBN a ranar 2 ga watan Yuni, 2014 zai kare zangonsa na farko a ranar 2 ga watan Yuni na wannan shekarar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa ga majalisar dattawa inda ya nemi a tabbatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN karo na biyu na tsawon shekaru biyar.

KU KARANTA KUMA: Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Idan aka tabbatar da shi, Emefiele zai zamo gwamnan CBN na farko da ya riki mukaamin sau biyu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan, ya nemi Sanatoci su fara shirin tantance gwamnan na CBN da yake karanto jeringiyar aikin da ke gaban majalisar a ranar. Bukola Saraki ya nemi a mika wannan batu zuwa kwamiti.

Shugaban majalisar, yace wannan kwamiti zai yi bincike a kan zargin da ke yawo a kan wuyar gwamnan mai-ci. Bukola Saraki yace duk da shugaban kasa ya zabi Emefiele, majalisa za ta tsaya ta duba duk zargin laifin da ke kan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel