Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a yau Laraba, 15 ga watan Mayu a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ma ya halarci zaman wanda ke kan gudana a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Sauran mutanen da suka hallara sun hada da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Abba Kyari da kuma ministoci.

Ga hotunan zaman a kasa:

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
Source: Facebook

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Shugaba Buhari yayinda yake jagorantar zaman majalisar zartarwa
Source: Facebook

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ma ya hallara
Source: Facebook

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
Source: Facebook

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba zai iya tabbatar da cewa ko azumin Ramadana yayi tasiri akan halayen ministan labarai, Lai Mohammed, ministan ilimi, Adamu Adamu da kuma Shugaban ma’aikatan Buhari, Abba Kyari ba.

KU KARANTA KUMA: Babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta wanda sauran kasashe basa fuskanta – Lai Mohammed

Osinbajo wanda yayi Magana a lokacin da Buhari ya gayyace shi da wasu ministoci shan ruwa a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, yace wasu dalilai sun sanya shi duba izuwa ga watan Ramadan amma sai ya tarar da akasin haka a lokacin da aka shiga watan.

Osinbajo yace wani kalubale kuma shine cewa Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa mafi tsawo a tarihi a wannan watan na Ramadana.

Yace yana ta duba zuwa Ramadan saboda taron majalisa kan kasance a gajere a watan amma “kada mu kuma sanya ran cewa zaman majalisar na iya zama gajere a watan Ramadan."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel