Babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta wanda sauran kasashe basa fuskanta – Lai Mohammed

Babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta wanda sauran kasashe basa fuskanta – Lai Mohammed

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed yace yawan yada labaran karya ya fara bayar da tsro sannan kuma ya shafi martabar kasar a idon duniya.

Ministan wanda ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da tashar Aso Television (TV) da Aso Radio a ranar Talata, 14 ga watan Mayu ya kuma bayyana cewa “babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta a yau da sauran kasashe basa fuskanta.”

Yayi kira ga kwararru a harkar watsa labarai da su tashi su kalubalanci lamarin sannan su sanya ra’ayin kasa a gaba da komai.

Babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta wanda sauran kasashe basa fuskanta – Lai Mohammed

Babu wani kalubale da Najeriya ke fuskanta wanda sauran kasashe basa fuskanta – Lai Mohammed
Source: Facebook

“Muna so mu kalubalanci yan jaridunmu kan su san cewa watsa labaran karya a yau, yana shafar martabarmu a idanun duniya.

“Ba zai yiwu ka shafa wa kasarka bakin fentin cewa tana da sugaba da ya gaza sannan ka sanya ran a mutunta kasar a duniya ba.

“Ba wai muna neman hana yada bayanai bane ko kuma tauye hakkin kafofin watsa labarai ba.

“Muna rokon kafofin watsa labarai da su daidaita kansu idan ba haka ba kuma za su lalata kansu.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Dakarun NAF sun kashe 'yan bindiga 12, sun kubutar da mutane 15 a dajin Kaduna

“Martabar wannan kasa na sauka saboda labaran karya kuma haka babban hatsari ne ga hadin kanmu.

“Najeriya ce a gaba da ra’ayin kowa saannan ya zama dole muyi aiki wajen kare martabar wannan kasa. Najeriya ta zo a aban komai,” inji shi.

Ministan ya kara da cewa da taimakon matakai da aka gabatar a gaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dukkann wadannan kalubale zai zama tsohon labara a nan gaba kadan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel