Kotu ta dakatar da EFCC, DSS, CCT da sauransu daga gudanar da sabon bincike akan Saraki

Kotu ta dakatar da EFCC, DSS, CCT da sauransu daga gudanar da sabon bincike akan Saraki

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Sufeto-Janar na yan sanda da wasu uku daga ci gaba da sabonta bincikensu akan Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Hakazalika daga cikin wadanda umurnin dakatar da bincike da Justis Taiwo Taiwo ya bayar a ranar Talata ya shafa sun hada da hukumar yan sandan farin kaya (DSS), hukumar ICPC da kotun CCT.

Justis Taiwo ya bayar da umurnin ne a hukunci biyu da ta yanke akan karar da Saraki da hukumomin kare hakkin dan adam biyu suka shigar masu lamba FHC/ABJ/CS/507/2019 da FHC/ABJ/CS/508/2019.

Kotu ta dakatar da EFCC, DSS, CCT da sauransu daga gudanar da sabon bincike akan Saraki

Kotu ta dakatar da EFCC, DSS, CCT da sauransu daga gudanar da sabon bincike akan Saraki
Source: Depositphotos

A cewar alkalin, umurnin ya kasance kokari na kammala sauraro da yanke hukunci akan karar da take hakki biyu da Saraki ya shigar.

KU KARANTA KUMA: Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

Lauyan Saraki, Sunday Onubi, yace idan ba wai an dakatar da sabon binciken bane, wanda ake karan za su tauye hakkin wanda ke karan kafin a saurari karar da ya shigar.

Justis Taiwo ya sanya ranar 23 ga watan Mayu domin sauraron shari’an.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayi duba I zuwa ga irin rashin jituwa da aka yi ta samu tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokokin Najeriya, inda ya karkare cewa anyi mugun zama da juna, kuma bai ji dadin hakan ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya gayyaci shuwagabannin majalisar, Sanata Bukola Saraki da Kaakakin majalisa Yakubu Dogara zuwa fadar gwamnati domin zaman buda baki tare dashi a daren Talata, inda yace zaman da suka yi da juna bai kamata ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel