An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Da safiyar ranar Laraba ne kotun sauraron korafin zabe shugaban kasa ta cigaba da zama domin cigaba da sauraron karar da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar domin kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Malam Nuhu Ribadu, ne ke wakiltar shugaba Buhari a zaman kotun, yayin da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ke wakiltar Atiku.

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC
Source: Twitter

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Cikin zauren kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC
Source: Twitter

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Jami'an tsaro a wajen kotun
Source: UGC

An cigaba da zaman kotun sauraron karar da Atiku da PDP suka shigar da Buhari da APC (Hotuna)

Jami'an tsaro a hanyar zuwa kotun
Source: UGC

Shugabar kotun daukaka kara ta kasa, Jastis Zainab Bulkachuwa, ce ke jagorantar kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa.

Jim kadan bayan zaman kotun, jam'iyyar PDP ta bukaci ganin shugabar tawagar alkalan kotun da ragowar mukarrabanta a dakin ganawa. Manyan lauyoyi biyu daga kowanne bangare za su kasance tare da alkalan a dakin ganawar.

DUBA WANNAN: Buratai ya yi banbami a kan mutuwar babban soja da wasu kananan sojoji a Borno

An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewaye domin nesanta wasu magoya bayan jam'iyyar PDP daga harabar kotun bisa zargin zasu gudanar da zanga-zanga.

A ranar Litinin ne wasu magoya jam'iyyar ta PDP suka gudanar da zanga-zanga nuna rashin amincewa da kasancewar Jastis Bulkachuwa a matsayin alkaliyar dake jagorantar kotun sauraron karar zaben shugaban kasa bisa zargin cewar mijinta zababben sanata ne a jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel