Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi

Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi

- Dubun wani mutumi ta cika yayin da kotu ta yanke mishi hukunci, bayan ta kama shi da yiwa 'yar gidan makwabcinsa fyade har sau uku

- Mutumin ya sanar da bakinsa cewa sau uku yana kwanciya da yarinyar makwabcin nasa, wacce ta ke da shekaru uku a duniya

A jiya Talata 14 ga watan Mayu, 2019, kotu ta tura wani mutumi dan shekara 40, mai suna Sani Ibrahim, gidan yari bayan ta kama shi da laifin yiwa yarinyar makwabcinsa fyade.

Ibrahim, wanda zai kasance a gidan kurkuku har zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2019, kotu na tuhumar sa da aikata fyade a karkashin sashe na 283 na dokar kasa.

Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi

Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi
Source: UGC

Wani jami'in dan sanda ya bayyanawa kotu cewa, mahaifin yarinyar, Hamisu Lawali, shine ya kawo karar lamarin a ofishin 'yan sanda na Bindawa, ranar 9 ga watan Mayu, kasa da sa'o'i biyu bayan an kama Ibrahim lokacin da yake yiwa yarinyar fyade.

KU KARANTA: Majalisar dokokin Najeriya ta amince da wani kuduri akan Jakuna

Ibrahim, Lawali da yarinyar da aka yiwa fyaden, duk mazauna unguwar Sabuwa Abuja ne dake karamar hukumar Bindawa cikin jihar Katsina. Lawali ya bayyanawa 'yan sanda cewa ba wannan ne karo na farko da Ibrahim ya aikata laifin ba.

A bayanin da dan sandan ya bayar, ya bayyanawa Kotun Majistire ta Katsina, cewa bayan an binciki Ibrahim, ya bayyana cewa ya kwanta da yarinyar har sau uku.

Ba wannan ne karo na farko da kotu ta ke yin hukunci akan irin wannan lamari na fyade ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel