Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

- Biyar daga cikin zababbun sanatocin APC 64 sun nuna ra’ayinsu na neman takarar kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa

- Tuni yan takarar suka fara tattaunawa da kamfen akan kudirinsu

- Yan takarar sun kaddamar da kamfen dinsu ta hanyar kamun kafa da sanatocin APC da na jam’iyyar adawa ta PDP

Wani rahoto daga jaridar ThisDay ya nuna cewa biyar daga cikin zababbun sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki 64 sun nuna ra’ayinsu na neman takarar kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa a majalisar dokokin kasar na tara yayinda ake shirin rantsar da ita a watan Yuni.

A cewar rahoton, wadanda ke zawarcin karbam matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa daga hannun sanata Ike Ekweremadu sun hada da manyan sanatoci irinsu Kabiru Gaya (arewa maso yamma), Francis Alimikhena (kudu maso kudu), Ovie Omo-Agege (kudu maso kudu), Ajayi Boroffice (kudu maso yamma) da kuma zababben sanata a karo na farko Orji Uzor-Kalu (kudu maso gabas).

An tattaro cewa yan takarar sun fara tattaunawa da kamfen a tsakanin tsoffin sanatoci da sabbi domin cimma kudirinsu.

Majiyoyi sun rahoto cewa yan takarar sun kaddamar da kamfen din nasu ne ta hanyar kamun kafa da zababbun sanatocin APC da kuma na jam’iyyar adawa wato Peoples Democratic Party (PDP) sannan suna bayyana dalilin da yasa suka cancanci a zabe su.

Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)
Source: Twitter

Daya daga cikin yaan takarar, sanata Boroffice (Ondo ta arewa) a bangarensa, ya rubuta wasika ga dukkanin zababben sanatoci inda yake neman goyon bayansu a matsayin mataimakin Shugaban majalisar.

Gaya (Kano ta kudu), shine na farko da ya fara kaddamar da ra’ ayinsa jim kada bayan sake zabarsa a watan Maris, ya kasance a majalisa tun 2007 kuma shine Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan ayyuka.

KU KAARANTA KUMA: Dan Allah ku yafe mani kura-kuraina – Bindow ya roki mutanen jihar Adamawa

Alimikhena (Edo ta arewa), wanda ya kasance mataimakin Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan gidaje kuma wanda ya dawo a karo na biyu, na ta kamun kafa don samun kuri’un takwarorinsa.

A nashi bangaren, Omo-agege, wanda ya lashe zabe a 2015 karkashin jam’iyyar the Labour Party (LP) kafin ya koma APC a 2016, ya samu goyon bayan shugabannin APC na yankin kudu maso kudu a makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel