Angulu ba zata koma gidanta na tsamiya ba – Inji gwamnan APC daya koma PDP

Angulu ba zata koma gidanta na tsamiya ba – Inji gwamnan APC daya koma PDP

Gwamnan jahar Benuwe, Samuel Ortom ya bayyana rahoton da wasu ke yadawa game da yiwuwar komawarsa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC a matsayin labaran kanzon kurege, kamar yadda jaridar Blue Print Newspaper ta ruwaito.

Ga masu bibiyan shafin Legit.ng suna sane da cewa mun kawo muku rahoton sauyin shekar Gwamna Samuel Ortom a shekarar data gabata, inda ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki ya koma jam’iyyar PDP, daga bisani ya sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu a PDP, kuma ya kai labari.

KU KARANTA: Gasar zakarun nahiyar Afirka: Najeriya ta fitar da zaratan yan wasan da zasu wakilceta

Sai dai jita jitan da ake yadawa na kwana kwanan nan baya rasa nasaba da ziyarar da gwamnan ya kai ma shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda hakan yasa ya kasance daya daga cikin yan sahun farko da suka fara ganawa da Buhari tun bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya inda ya kwashe kwana 10.

Kaakakin gwamnan, Terver Akase ya musanta rahoton, inda yace gwamnan na zaman lafiya tare da kulla kyakkyawar alaka tsakaninsa da sauran shuwagabannin jam’iyyar PDP dake fadin jahar Benuwe dama kasa baki daya, don haka babu maganan ficewa daga PDP.

Game da ziyarar daya kai fadar shugaban kasa kuwa, gwamnan yace ya kai wannan ziyara ne domin tattauna da shugaba Buhari game da matsalolin da suka mamaye jahar Benuwe, musamman matsalar tsaro, da kuma kokarin da yake yi don shawo kan matsalar.

“Don haka muna kira ga masu watsa wannan jita jita dasu sani shugaba Buhari ba shugaban APC bane kawa, shugaban dukkanin yan Najeriya ne, kuma shine babban kwamandan askarawan Sojan Najeriya, hakan yasa duk gwamnoni suna kai masa rahoto.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel