Dan Allah ku yafe mani kura-kuraina – Bindow ya roki mutanen jihar Adamawa

Dan Allah ku yafe mani kura-kuraina – Bindow ya roki mutanen jihar Adamawa

- Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow ya nemi yafiya daga mutanen jihar Adamawa

- Gwamnan yace ya san yayi wa wasu mutane laifi a shekaru hudu da yayi akan mulki

- Bindow ya kuma bayyana cewa shugabantar jihar ya kasance abu mai wahala gare shi

Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow na jihar Adamaw ya bayyana jagorantar jihar a matsayin aiki mai wahala, inda ya kara da cewa ya san babu mamaki yayi wa wasu mutane laifi wanda yana barar yafiya daga gare su.

Jaridar The Nation ta raahoto cewa yayinda yake bayar da jawabin da za a iya kira da jawabin bankwana a wasu taro daban-daban a Yola, Bindow ya bukaaci a yafe masa kura-kuransa a wannan wata na Ramadana.

Legit.ng ta tattaro cewa Bindow wanda ya kasance gwamnan jihar tun a shekarar 2015, ya fadi a neman tazarcensa a watan Maris, don haka zai bar kujerar gwamnati a wannan watan.

Dan Allah ku yafe mani kura-kuraina – Bindow ya roki mutanen jihar Adamawa
Dan Allah ku yafe mani kura-kuraina – Bindow ya roki mutanen jihar Adamawa
Source: Facebook

A wani taro da aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnati inda ya kaddamar da sabon shirin inshoran lafiya na jihar Adamawa, Bindow yace, “Ban sani ba, amma tabbass, mutane da dama sun yarda cewa shugabantar Adamawa abu ne mai wuyan fahimta. Bai zo da sauki ba, amma nayi iya bakin kokari na a wadannan shekaru.”

KU KARANTA KUMA: Madalla: Al’umman jihar sokoto sun samu ruwan sama na farko

Gwamnan wanda ya kaddamar da shirin tare da mataimakinsa, Martins Babale, yace abu guda da zai yi kewa sosai bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, shine alakar aiki da ke tsakaninsa da mataimakinsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel