Kwamitin Sanatoci za su dirje Godwin Emefiele kafin ya koma ofis

Kwamitin Sanatoci za su dirje Godwin Emefiele kafin ya koma ofis

Ku na da labari cewa ‘Yan majalisa za su yi zaman a musamman kafin su amince da karin wa’adin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake so ayi wa gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

A jiya Talata 14 ga Watan Mayun 2019, majalisar dattawa ta bijriro da maganar sake karawa Godwin Emefiele wa’adin shekaru 5 a CBN. Sanatoci za su zauna a kan batun tazarcen gwamna na CBN ne kamar yadda dokar kasa ta bada dama.

A zaman jiya, shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan, ya nemi Sanatoci su fara shirin tantance gwamnan na CBN da yake karanto jeringiyar aikin da ke gaban majalisar a ranar. Bukola Saraki ya nemi a mika wannan batu zuwa kwamiti.

A halin yanzu, kwamitin da ke kula da sha’anin banki da inshora ne zai zauna domin ganin cewa ko Godwin I. Emefiele ya dace ya koma ofis a matsayin gwamnan CBN ko kuwa. Sanata Rafiu Adebayo Ibrahim ne shugaban wannan kwamiti.

KU KARANTA: CBN: Shugaban Majalisa ya karanta wasikar Buhari

Kwamitin Sanatoci za su dirje Godwin Emefiele kafin ya koma ofis
Kwamitin sha’anin banki zai binciki Godwin Emefiele a Majalisa
Asali: UGC

Shugaban majalisar, yace wannan kwamiti zai yi bincike a kan zargin da ke yawo a kan wuyar gwamnan mai-ci. Bukola Saraki yace duk da shugaban kasa ya zabi Emefiele, majalisa za ta tsaya ta duba duk zargin laifin da ke kan sa.

Rafiu Adebayo Ibrahim da sauran ‘yan kwamitin na sa, za su yi sauri wajen ganin an amince da nadin na Godwin Emefiele ko kuma su yi watsi da shi, ganin yadda lokaci ya kai ya kawo. Wa’adin Emefiele zai kare ne a Ranar 2 ga Watan Yuni.

Sashe na 8(1) da na 2 na dokokin CBN ya nemi majalisa ta tantance wanda shugaban kasa ya zaba a matsayin gwamnan babban bankin kasar. Bayan kwakmiti sun yi aikin su, za su kawo rahoto gaban zauren majalisa domin a tattauna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel