Gasar zakarun nahiyar Afirka: Najeriya ta fitar da zaratan yan wasan da zasu wakilceta

Gasar zakarun nahiyar Afirka: Najeriya ta fitar da zaratan yan wasan da zasu wakilceta

Babban mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr ya fitar da sunayen zaratan yan kwallon kafa da zasu wakilci Najeriya a gasar taka leda da za’ayi a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka na shekarar 2019.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata 14 ga watan Mayu ne Rohr ya fitar da sunayen yan kwallon guda 25, sa’annan ya dawo da dan wasan tsakiya Mikel Obi cikin tawagar yan kwallon a matsayin jagoran yan wasa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Manyan hakiman fadar Sarkin Kano guda 4 sun nuna ma Ganduje yatsa

Gasar zakarun nahiyar Afirka: Najeriya ta fitar da zaratan yan wasan da zasu wakilceta
Yan wasan
Source: UGC

Ga dai jerin sunayen zaratan yan kwallon nan da kungiyoyin da suke taka leda kamar hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta fiddasu;

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Ikechukwu Ezenwa (Katsina United); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa)

Masu tsaron gida: Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy); Abdullahi Shehu (Bursaspor FC, Turkey); Chidozie Awaziem (Caykur Rizespor, Turkey); William Ekong (Udinese FC, Italy); Leon Balogun (Brighton & Hove Albion, England); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany); Semi Ajayi (Rotherham United, England)

Yan wasan tsakiya: Mikel John Obi (Middlesbrough FC, England); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (Stoke City FC, England); John Ogu (Hapoel Be’er Sheva, Israel)

Yan wasan gaba: Ahmed Musa (Al Nassar FC, Saudi Arabia); Victor Osimhen (Royal Charleroi SC, Belgium); Moses Simon (Levante FC, Spain); Henry Onyekuru (Galatasaray SK, Turkey); Odion Ighalo (Shanghai Shenhua, China); Alexander Iwobi (Arsenal FC, England); Samuel Kalu (Girondins Bordeaux, France); Paul Onuachu (FC Midtjyland, Denmark); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain)

Sai kuma masu kafa daya a ciki kafa daya a waje guda 6: Theophilus Afelokhai (Enyimba FC); Bryan Idowu (Lokomotiv Moscow, Russia); Ikouwem Utin (Enyimba FC); Mikel Agu (Vitoria Setubal, Portugal); Junior Ajayi (Al Ahly, Egypt); Valentine Ozornwafor (Enyimba FC).

Mai horas da kungiyar ya umarci dukkanin yan wasan dasu hallara Otal din Golden Tulip dake garin Asaba na jahar Delta a ranar 2 ga watan Yuni don samun damar fafatawa a wasan sada zumunta da kasar Zimababwe a ranar 8 ga watan Yuni.

Daga jahar Delta kungiyar kwallon kafa ta Najeriya zata wuce kasar Masar domin fara atisaye a sansaninta dake jahar Ismailia, sa’annan su sake karawa da kasar Sanigal a wasan sada zumunci a ranar 16 ga watan Yuni.

Najeriya zata fuskanci kasashen Burundi, Guinea da Madagascar ne a rukunin B na gasar na bana, wanda shine gasa na 32 a jerin gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel