Mutanen Kwara su na so Lai ya cigaba da zama Minista a Najeriya

Mutanen Kwara su na so Lai ya cigaba da zama Minista a Najeriya

Mun samu labari cewa wasu ‘Yan jam’iyyar APC a jihar Kwara sun nuna cewa za su so ace Lai Mohammed ya cigaba da rike kujerar Minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta rahoto cewa wata kungiya ta ‘Ya ‘yan APC da ke cikin karamar hukumar Irepodun a jihar Kwara, sun nemi shugaban kasa Buhari ya cigaba da aiki da Alhaji Lai Mohammed, wanda shi ne Ministan yada labarai a yanzu.

Shugaban wannan kungiya, Dr. Hezekiah Oyedepo, ta yabawa Ministan kasar inda tace yayi abin a-yaba a kan kujerar da yake kai na Ministan yada labarai da kuma ala’adu da duk sauran kujerun da ya saba rikewa a tarihin siyasarsa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya furta da kan sa cewa ana fama da talauci

Mutanen Kwara su na so Lai ya cigaba da zama Minista a Najeriya
Hezekiah Oyedepo tace ya kamata Buhari ya koma da Lai
Source: Depositphotos

Hezekiah Oyedepo ta bayyana wannan ne a lokacin da ta tara ‘yan jarida a Garin Ilorin a Ranar 13 ga Watan Mayu. Oyedepo take cewa Ministan yayi kokarin gaske wajen samun nasarar jam’iyyar APC a jihar Kwara a zaben da ya gabata.

Wannan Baiwar Allah mai jagorantar kungiyar APC a Garin Irepodun ta kuma ce Lai Mohammed ya jawowa jihar Kwara da kuma yankinsa ayyukan da-dama a sanadiyyar amfani da kujerarsa da ya rika yi a wannan gwamnati ta APC.

Kungiyar take cewa mutane sun amfana da irin rawar ganin da tsohon Kakakin na APC ya samu bayan ya shiga gwamnati, don haka su ke rokon APC ace yana cikin wadanda Buhari zai sake nadawa a cikin gwamnatinsa wannan karo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel